Isa ga babban shafi

CAF zata tantance gwarzo tsakanin Salah, Aubmeyang da Mane

Shahararrun 'yan wasan kwallon kafa daga nahiyar Africa Salah, Mane da kuma Aubameyang, wadanda hukumar CAF ta zaba domin tantance wanda zata mikawa kyautar gwarzon dan wasan Afrika.
Shahararrun 'yan wasan kwallon kafa daga nahiyar Africa Salah, Mane da kuma Aubameyang, wadanda hukumar CAF ta zaba domin tantance wanda zata mikawa kyautar gwarzon dan wasan Afrika. Daily Guide Africa

Hukumar CAF ta zabi ‘yan takara uku na karshe da zata zabi gwarzon dan wasan Afrika, wadanda suka hada da, dan kasar Masar wato Mohammed Salah, na kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Sadio Mane na kasar Senegal da ke kungiyar Liverpool, sai kuma Pierre-Emerick Aubameyang dan kasar Gabon, da ke kungiyar Borussia Dortmund.

Talla

A bangaren mata kuwa 'yar wasan Super Falcons ta Najeriya, Azizat Oshoala, da ta lashe kyautar gwarzuwar ‘yar wasan nahiyar Afrika a shekarun 2014 da 2016, na daga cikin ‘yan wasa uku da aka zabo na wannan shekara, tare da Gabrielle Aboud ta kasar Kamaru, da kuma Chrestina Kgatlana ta Afrika ta Kudu.

A bangaren masu horarwa kuwa, za’a tantance gwarzo ne tsakanin kocin Najeriya Genort Rohr, Hector Cuper mai horar da kasar Masar da kuma L’Hussein Amoutta mai horar da kungiyar Wydad Casablanca da ke kasar Morocco.

A gefen tawagar kwallon kafa mafi kwarewa a matakin kasa kuwa, za’a tantance ne tsakanin Super Eagles na Najeriya, Kamaru da kuma tawagar kwallon kafa ta kasar Masar.

Za’a gudanar da wannan zabe ne a birnin Accra, Ghana, ranar 4 ga watan Janairu mai zuwa.

Sai dai rashin sunan dan Najeriya bai yi wa tsaffin 'yan wasan Najeriya Taribo West da Victor Agali dadi ba, inda suka ce bai cancanci a cire sunan Victor Moses dan wasan gaba na Najeriya, daga cikin jerin ‘yan wasan nahiyar Afrika 3, da za’a zabi gwarzon wannan shekara ta 2017.

A cewar su Taribo West, Victor Moses ya cancanci fitowa cikin ‘yan wasan uku da za’a tantance, saboda yadda tauraruwarsa ke haskawa a kungiyarsa ta Chelsea da kuma gida Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.