Isa ga babban shafi
wasanni

Morocco ta lashe kofin CHAN bayan ta doke Najeriya

Tawagar kwallon kafar Morocco ta Atlas Lion na murnar lashe kofin CHAN ta 2018
Tawagar kwallon kafar Morocco ta Atlas Lion na murnar lashe kofin CHAN ta 2018 FADEL SENNA / AFP

Tawagar kwallon kafa ta Morocco ta lashe gasar cin kofin Afrika ta ‘yan wasan da ke taka leda a gida wato CHAN bayan ta lallasa Najeriya da ci 4-0 a wasan karshe da suka fafata a jiya a Casablanca.

Talla

Yanzu haka Morocco ta shiga sahun kasashen Jamhuriyar Demokradiyar Congo da Tunisia da Libya da suka taba lashe wannan kofin.

Dan wasan Morocco Ayoub El Kabi ya taka gagarumar rawa a nasarar da kasar ta samu, in da aka ayyana shi a matsayin gwarzon gasar baki daya, yayin da ya fi kowa zura kwallaye a gasar ta bana, in da ya ke da kwallaye 9.

Sakamakon rawar da ya taka, ana ganin watakila kocin tawagar Morocco, Herve Renard zai ba shi damar buga wa kasar gasar cin kofin duniya da Rasha za ta karbi bakwanci a bana, in da za su kara da Iran da Portugal da Spain.

Baya ga kofin na CHAN da Morocco ta lashe, har ila yau, an bai wa ‘yan wasan kyautar Dalar Amurka miliyan 1.25.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.