Isa ga babban shafi
wasanni

Moses ya lashe kyautar gwarzon dan wasan Najeriya

Victor Moses ya taimaka wa Najeriya samun gurbi a gasar cin kofin duniya a Rasha
Victor Moses ya taimaka wa Najeriya samun gurbi a gasar cin kofin duniya a Rasha Reuters

Dan wasan Najeriya da ke taka leda a Chelsea, Victor Moses ya lashe kyautar gwarzon dan wasan shekara a wani kasaitaccen biki da hukumar kwallon kafar kasar ta gudanar a jihar Legas a yammacin jiya Litinin.

Talla

Moses ya samu kyautar ce bayan doke Wilfred Ndidi na Leicester City da Anthony Okpotu na Lobi Star da suka fafata wajen lashe kyautar.

Moses mai shekaru 27 ya taimaka wa Chelsea lashe kofin firimiyar Ingila a bara, sannan ya kasance daya daga cikin zaratan ‘yan wasan Najeriya da suka nema wa kasar gurbi a gasar cin kofin duniya a Rasha, in da ya zura kwallaye uku a wasanni hudu da ya yi wa kasar a gasar neman gurbi a Rasha.

A bangaren mata kuwa, Asisat Oshiola ce ta lashe kyautar gwarzowar ‘yar wasan shekara a bikin, wanda ya samu halartar shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, Gianni Infatino da shugaban hukumar kwallon kafar Afrika, Ahmad Ahmad da Sakatariyar FIFA, Fatma Samoura da gwamnan jihar Legas, Akinwumi Ambode.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.