Isa ga babban shafi
Wasanni

FIFA ta fara bincike akan cin zarafin 'yan wasan Faransa a Rasha

Dan wasan Faransa Paul Pogba, yayin wasan sada zumuncin da suka lallasa kasar Rasha da kwalaye 3-1.
Dan wasan Faransa Paul Pogba, yayin wasan sada zumuncin da suka lallasa kasar Rasha da kwalaye 3-1. Reuters

Hukumar FIFA a Rasha ta fara bincike kan matsalar nuna wariyar launin fata da ta kunno kai a fagen wasanni a Rasha, yayin da ya rage makwanni kadan a fara gasar cin kofin duniya a watan Yuni.

Talla

Binciken ya biyo bayan yadda wasu ‘yan kasar a ranar Talata da ta gabata suka ci zarafin ‘yan wasan Faransa, Paul Pogba da Ousmane Dembele, a lokacin wasan sada zumuncin da Faransa ta lallasa Rasha da kwallaye 3-1 a Saint Petersburg.

Da fari dai wani mai daukar hoton kamfanin dillancin labaran Faransa AFP ne ya rawaito cewa tabbas yaji wasu ‘yan kasar ta Rasha suna yin sauti irin na Biri, da nufin cin zarafin Pogba da kuma Dembele, daga sassa daban daban na akalla masu kallo dubu 50,000 da suka halarci wasan sada zumuncin.

‘Yan wasa musamman bakaken fata sun dade suna fuskantar wannan matsala ta nuna wariyar launi a Rasha, inda a mafi akasarin lokuta, wasu daga cikin ‘yan kasar ke yi musu sautuka irin ba Biri, ko kuma su rika jifarsu da bawon ayaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.