Isa ga babban shafi
Wasanni

Serena zata fafata wasan farko a Grand Slam bayan hutun jego

Serena Williams bayan lashe gasar Grand slam ta Australian Open a watan Janairun 2017, kofi na 23 da ta lashe a manyan wasannin da ta buga a tarihinta.
Serena Williams bayan lashe gasar Grand slam ta Australian Open a watan Janairun 2017, kofi na 23 da ta lashe a manyan wasannin da ta buga a tarihinta. REUTERS/Edgar Su

Tsohuwar lamba daya a fagen wasan kwallon Tennis Serena Williams zata fafata wasan zagayen farko na gasar French Open da Kristyna Pliskova ‘yar Jamhuriyar Czech.

Talla

A jiya Alhamis masu shirya wasan Tennis din na French Open suka fitar da tsarin jadawalin yadda wasan zagayen farkon zai kaya.

Karo na farko kenan da Serena Williams tsohuwar lamba daya a wasan tennis din a duniya zata buga wasan da ake wa lakabi da Grand Slam, a dai dai lokacin da a yanzu matsayinta ya koma ta 453 a tsakanin ‘yan wasan ne kwallon Tennis a duniya ajin mata.

Bayan lashe kofin gasar Australian Open a 2017, kofi na 23 daga wadanda ta lashe a gasa daban daban da ta buga, Serena Williams ta fi hutun haihuwa, inda ta sauka a watan Satumba.

A nata bangaren wadda zata fafata da Serena, Pliskova yar wasan tennis ta 70 a duniya, bata taba lashe wani babban wasa ba a gasar ta French Open ko Roland Garros.

A halin yanzu ‘yan wasan tennis mafi shara ajin mata a duniya sun hada da, Simona Helep ‘yar kasar Romania a matsayin ta 1, Caroline Wozniacki ta Denmark a matsayi na 2.

Garbiñe Muguruza Blanco ‘yar Spain ke a matsayin 'yar wasan tennis ta 3 mafi kwarewa a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.