Isa ga babban shafi
Wasanni

Babu wata barazanar tsaro da za ta yi tasiri yayin wasanni - Rasha

Shugaban hukumar samar da tsaro yayin gasar cin kofin duniya a Rasha, Alexei Lavrishchev.
Shugaban hukumar samar da tsaro yayin gasar cin kofin duniya a Rasha, Alexei Lavrishchev. AFP / Yuri KADOBNOV

Rasha ta sanar da daukar matakan murkushe duk wata barazanar tsaro da aka iya tasowa yayin gudanar da gasar cin kofin duniya da za ta karbi bakunci.

Talla

A karshen watan Mayu, ma’ikatar tsaron kasar ta sanar da girke wasu na’urori a filayen da za a buga wasannin gasar cin kofin duniyar, irin wadanda da aka yi amfani da su a yake-yaken kasashen Syria da Ukraine, don bada kariya ga filayen wasannin daga yiwuwar kai hare-haren ta’addanci.

Sai dai har yanzu ma’aikatar cikin gidan kasar ta Rasha, bata bayyana adadin jami’an tsaron da za a girke domin sintiri yayin gudanar gasar ta cin kofin duniya.

Akalla mutane 600, 000 daga kasashen duniya ake sa ran zasu halarci kallon gasar cin kofin duniyar da za a soma ta a mako mai kamawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.