Isa ga babban shafi
Wasanni

Roland Garros: Saharapova ta sha kaye mafi muni cikin shekaru 6

Garbine Muguruza 'yar kasar Spain a bangaren dama, a lokacin da Maria Sharapova ta Rasha da ke bangaren hagu, ke yi mata murnar kai wa wasan kusa da na karshe a gasar Roland Garros.
Garbine Muguruza 'yar kasar Spain a bangaren dama, a lokacin da Maria Sharapova ta Rasha da ke bangaren hagu, ke yi mata murnar kai wa wasan kusa da na karshe a gasar Roland Garros. AFP

Garbine Muguruza ‘yar kasar Spain samu kaiwa ga zagayen kusa da na karshe a gasar kwallon tennis ta French Open ko Rolland Garros da ke gudana a Faransa.

Talla

Muguruza shahararriyar ‘yar kwallon tennis ta 3 a duniya, ta samun nasarar ce, bayan da ta lallasa Maria Sharapova ta Rasha da kwallaye 6-2, da kuma 6-1, a wasan da suka fafata a ranar Laraba.

Wannan rashin nasara ita ce mafi muni da Sharapova, ‘yar kwallon tennis ta 30 a duniya ta taba fuskanta cikin sama da shekaru 6.

A ranar Asabar mai zuwa, Garbine Muguruza wadda ta taba lashe kofin gasar Roland Garros din a shekarar 2016, zata fafata wasan kusa da na karshen ne da Simona Halep ‘yar kasar Romania kuma lamba daya a fagen kwarewar kwallon tennis a duniya ajin mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.