Isa ga babban shafi
Wasanni

FIFA za ta zabi kasar da za ta karbi bakuncin gasar 2026

Shalkwatar hukumar FIFA ta Duniya a birnin Zurich
Shalkwatar hukumar FIFA ta Duniya a birnin Zurich REUTERS/Arnd Wiegmann/Files

A Jajibirin soma gasar cin Kofin kwallon kafa ta Duniya da za’a yi a kasar Rasha ne hukumar FIFA za ta zabi ko wace kasa ce za ta sami damar karbar bakuncin gasar 2026 tsakanin kasashen yankin Arewacin Amurka da na yankin Arewacin Afruka.

Talla

Yanzu haka ana maganar mai yuwa ne a gobe laraba, mambobin hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA su zabi wata kasa a yankin Arewacin Amurka ko kuma su zabi sake mai da gasar cin kofin kwallon kafa ta Duniya da za’a gudanar a 2026 a wata kasa ta Afruka a karo na biyu kuma Morocco ne ake hasashe idan har an maida wasar a yankin Nahiyar Afruka.

To amma kuma abin a fili yake, ko dai a zabi yankin Arewacin Amurka da suka hada da kasashen Mexico da Canada ko kuma a zabi mai fatar ganin ta samu dama wato Morocco wadda kuma filayen wasarta bakimtsatsu bane.

To ko ma dai miye a jajibirin wannan gasar ta 2018 ne kasashe mambobin hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA za su jefa kuri’ar zaben kasar da za ta kasance mai karbar bakluncin gasar ta 2026, sai dai kasar Morocco bata fara batun neman kuri’un mambobin ba sai a farkon wannan watan, kuma ita hukumar FIFA ta yi gargadin cewar akwai kasada amincewa da kasar ta Morocco da ke a yankin Arewacin Afrika saboda rashin manyan filayen wasa da masaukan baki, da hanyoyin sufuri da dai sauransu.

Amma dai kasashen na yankin Arewacin Amurka da suka hada da Mexico da Canada ne kan gaba a gasar neman damar idan aka yi la’akari da matsayin da suka samu na zama bagire mafi inganci idan aka kwatanta da kasar Morocco.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.