Isa ga babban shafi
Wasanni

Japan ta lallasa Colombia da ci 2 da 1

Tawagar 'yan kwallon Japan gabanin tunkarar Colombia a yau Talata.
Tawagar 'yan kwallon Japan gabanin tunkarar Colombia a yau Talata. REUTERS/Ricardo Moraes

Japan ta yi nasara kan Colombia da ci 2 da 1 matakin da ya bata damar zamowa kasa ta farko daga nahiyar Asiya da ta yi nasarar doke takwararta daga Latin Amurka.

Talla

Colombia dai ta karkare wasan na yau ne da ‘yan wasa 10 bayan da aka baiwa Carlos Sanchez jan kati.

Japan din ce ta fara zura kwallo ta hannun dan wasanta Shinji kagawa a minti na 6 da fara wasa kafin daga Juan Fernando ya farke a minti na 39 da fara wasa, inda kuma Yuya Osako ya kara a minti na 73 da fara wasa matakin da ya bai wa Japan din damar yin nasara kan Colombia.

Tun da aka fara wasannin na gasar cin kofin duniya wannan ne karon farko da wata kasa ta yi nasara kan kasashen Latin Amurka.

Ana ganin dai a wannan karon kasashen na Latin Amurka sun shigo gasar da karfinsu yayinda wasu ke ganin abu ne mai wuya idan guda daga cikin kasashen ba ta iya yin nasarar lashe kofin ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.