Isa ga babban shafi
Wasanni

Magoya bayan Juventus na rububin sayen rigar Ronaldo

Daya daga cikin magoya bayan kungiyar Juventus da suka yi rububin sayen rigar sabon dan wasansu Cristiano Ronaldo
Daya daga cikin magoya bayan kungiyar Juventus da suka yi rububin sayen rigar sabon dan wasansu Cristiano Ronaldo Yahoo Sports

Daruruwan magoya bayan kungiyar Juventus na ta yin tururuwa domin sayen riga mai dauke da lamba bakwai da kuma sunan Cristiano Ronaldo.

Talla

Magoya bayan sun dukufa wajen rububin ne, yayinda kungiyar ta Juventus ke shirin tabbatar da zuwan sauyin shekar Ronaldo zuwa gare ta a hukumance, ranar Litinin mai zuwa.

Kafin wannan lokaci dai, Juan Cuadrado ne ke sanyawa kungiyar lamba bakwai tun bayan sauyin shekar da ya yi daga Chelsea a shekarar 2015, amma halin yanzu hakan na nufin Cuadrado zai rasa lambarsa kenan sakamakon zuwan Ronaldo,

A farkon wannan mako, Juventus ta tabbatar da sayen Ronaldo daga kungiyar Real Madrid kan kudi euro miliyan 100, inda zai rika amsar albashin euro miliyan 30 a duk shekara, sabanin euro miliyan 23 da ya ke karba a Real Madrid.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.