Isa ga babban shafi
Wasanni

Ronaldo zai bugawa Juventus wasan farko a Chievo

Cristiano Ronaldo, yayin gaisawa da magoya bayan Juventus, bayan isa cibiyar kula da lafiya ta kungiyar da ke birnin Turin, a Italiya. 16 ga watan Yuli, 2018.
Cristiano Ronaldo, yayin gaisawa da magoya bayan Juventus, bayan isa cibiyar kula da lafiya ta kungiyar da ke birnin Turin, a Italiya. 16 ga watan Yuli, 2018. REUTERS/Massimo Pinca

A ranakun 18 da 19 na watan Agusta mai kamawa, Cristiano Ronaldo zai bugawa Juventus wasannin farko tun bayan sayenshi da kungiyar ta yi, daga zakarun kungiyoyin nahiyar turai Real Madrid, kan kudi euro miliyan 100.

Talla

Cikin sanarwar da kungiyar ta Juventus ta fitar, ta bayyana kwarin gwiwar cewa Ronaldo zai fitar da ita kunya a kakar wasa ta bana.

Wasannin da Ronaldo zai soma bugawa Juventus sun hada da tattakin da za yi domin ta fafata da kungiyar Chievo wadda ta tsallake rijiya da baya a kakar wasa ta bara, bayan ketara layin ajin ‘yan dagaji da kyar.

Wasa na biyu kuwa Juventus za ta karbi bakuncin Lazio a gida, inda ta shafe lokaci mai tsawo bata yi rashin nasara ba, a wasanninta na Seria A.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.