Isa ga babban shafi
Wasanni

Quadri ya lashe gasar kwallon tebur ta 'Nigeria Open'

Dan wasan kwallon tebur na Najeriya Quadri Aruna.
Dan wasan kwallon tebur na Najeriya Quadri Aruna. Anthony WALLACE / AFP

Dan Najeriya, Aruna Quadri ya lashe kofin gasar kwallon tebur ta ‘Nigeria Open’ wadda ta gudana a filin wasa na Teslim Balogun dfa ke birnin Lagos.

Talla

Quadri ya samu nasarar, bayan doke abokin karawarsa Antoine Hachard na Faransa da kwallaye 4-2.

Karo na farko kenan da dan Najeriyar ya lashe gasar, wadda hukumar kula da wasan kwallon tebur ta duniya ITTF ke shiryawa.

Dan Najeriyar wanda ke a matsayi na 18 a matakin kwarewa a fagen kwallon Tebur na duniya, ya samu kyautar dala dubu $5,000, sakamakon wannan nasara da ya samu.

A shekarar 2015, Aruna Quadri ya gaza lashe kofin gasar ta 'Nigeria Open', bayan shan kaye a hannun abokin hamayyarsa na kasar Masar, Omar Assar.

A bangaren mata kuma Guo Yan ‘yar kasar China ce ta lashe kofin kwallon tebur din, bayan lallasa takwararta Sun Chen da kwallaye 4-3.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.