Isa ga babban shafi
wasanni

Suarez ya dagula wa Real Madrid lissafi a El-Clasico

Luis Suárez ya jefa kwallaye uku a ragar Real Madrid a wasan El-Clasico
Luis Suárez ya jefa kwallaye uku a ragar Real Madrid a wasan El-Clasico REUTERS/Paul Hanna

Kungiyar Kwallon Kafa ta Barcelona ta lallasa babbar abokiyar hamayyarta wato Real Madrid da ci 5-1 a wasan da ake yi wa lakabi da El-Clasico a gasar La Liga a Spain, yayin da ake ganin da yiwuwar Madrid ta raba gari da kocinta.

Talla

Luis Suarez ya samu nasarar zura kwallaye uku shi kadai a ragar Madrid, yayin da Philippe Coutinho da Arturo Vidal kowannensu ya jefa guda-guda.

Tuni aka fara hasashen makomar kocin Madrid, Julen Lopetegui ganin yadda kungiyar ke fama da rashin karsashi a ‘yan kwanakin nan, in da jaridun Spain suka rawaito cewa, watakila a ranar Litinin a sallame shi daga bakin aiki, kuma ana kyautata zaton Antonio Conte ne zai maye gurbinsa.

Koda yake, Sergio Ramos ya shaida wa manema labarai cewa, kawo yanzu, babu wani bayani da suka samu daga mahukuntan Barcelona game da sauya kocin da wani bayan wannan lallarsa da Barcelona ta yi musu a Camp Nou.

Real Madrid ta samu nasara sau daya daga cikin wasanni shida da ta buga a baya-bayan nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.