Isa ga babban shafi
Wasanni

Modric ya lashe kyautar gwarzon dan wasa ta Ballon d'Or

Luka Modric ya kawo karshen shekaru 10 na Ronaldo da Messi wajen lashe kyautar gwarzon dan wasa ta Ballon d'Or.
Luka Modric ya kawo karshen shekaru 10 na Ronaldo da Messi wajen lashe kyautar gwarzon dan wasa ta Ballon d'Or. Goal.com

Luka Modric dan kasar Croatia dake kungiyar Real Madrid, ya lashe kyautar gwarzon dan wasan kwallon kafa na duniya ta Ballon d’Or.

Talla

Kyautar wadda aka yi bikin mika ta ga Modric daren jiya Litinin a birnin Paris, ta kawo karshen mamaye nasarar lashe ta hadi da ta gwarzon dan wasan FIFA da ‘yan wasa biyu, wato Cristiano Ronaldo da Lionel Messi suka shafe shekaru 10 suna yi.

‘Yan wasan da suka biyu bayan Modric sune Cristiano Ronaldo a matsi na biyu da kuma Antoine Griezmann a matsayi na uku.

A ajin mata kuwa, ‘yar wasan gaba ta kasar Norway Ada Hgerberg ce ta lashe kyautar gwarzuwar ‘yar kwallon kafa ta bana, wadda kuma ta kafa Tarihin zama wadda ta soma lashe kyautar Ballon d’Or ajin mata, kasancewar daga kanta aka soma bayar wa.

Hegerberg ta lashe kyautar ce la’akari da muhimmiyar gudunmawarta wajen nasarar kungiyarta ta Lyon ta yi na lashe gasar zakarun nahiyar Turai ajin mata.

A bangaren matasa kuwa, Kylian Mbappe na Faransa dake kungiyar PSG, ne yayi nasarar lashe sabuwar kyautar Ballon d’Or ta gwarzon dan kwallon kafa na duniya ajin ‘yan kasa da shekaru 21.

A gasar cin kofin duniya ta bana da aka yi a Rasha ma Mbappe ne ya lashe kyautar matashin dan wasa mafi kwazo, wanda cikin wannan wata zai cika shekaru 20.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.