Isa ga babban shafi
Wasanni

Ban gamsu da matsayin da Ballon d'Or ta baiwa Messi ba - Ernesto

Mai horar da Barcelona Ernesto Valverde da dan wasansa Lionel Messi.
Mai horar da Barcelona Ernesto Valverde da dan wasansa Lionel Messi. REUTERS/Albert Gea

Mai horar da kungiyar Barcelona Ernesto Valverde ya ce bai gamsu da matsayi na biyar da aka baiwa Messi ba a fagen gwarzayen ‘yan kwallon kafa na duniya, yayin bikin mika kyartar gwarzon dan wasa ta Ballon d’Or da aka yi ranar Litinin.

Talla

Valverde ya bayyana rashin gamsuwar tasa ce, yayin wata ganawa da manema labarai, sai dai ya ce babu amfanin bata lokacinsa wajen bayyana hujjojinsa kan haka, wadanda ya yi amanna cewar a bayyane suke.

A ranar Litinin da ta gabata Luka Modric dan kasar Croatia na Real Madrid ya lashe kyautar ta Ballon d’Or, wadda masu ruwa da tsaki kan harkar wasanni a Faransa ke bayarwa da aka kirkiro tun a shekarar 1956.

‘Yan jaridun da suka yi nutsu a fadgen wasanni 180 ne suka kada kuri’a wajen zaben zakaran na kyautar ta Ballon d’Or, inda Modric ya samu maki 753, sai Ronaldo mai maki 476 yayinda na Ukunsu Antoine Griezmann na Atletico Madrid yake da maki 414.

Kylian Mbappe na PSG ne a matsayi na 4 da maki 347, yayinda Messi ya samu maki 280 a matsayi na biyar.

Nasarar Modric dai ta kawo karshen shafe shekaru 10 da Lionel Messi da Criatiano Ronaldo suka yi suna lashe wannan kyauta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.