Isa ga babban shafi
Wasanni-kwallon kafa

An karrama Messi da kyautar takalmin zinare karo na 5

A cewar Messi bai tsammaci lashe kyautar takalmin na zinare har sau 5 ba a tarihinsa na Tamaula.
A cewar Messi bai tsammaci lashe kyautar takalmin na zinare har sau 5 ba a tarihinsa na Tamaula. Barcelonafc.com

An karrama dan wasan gaba na Argentina da ke taka leda a Barcelona mai doka gasar La liga, Lionel Messi yau Talata da kyautar takalmin zinare bayan zamowarsa dan wasa mafi zura kwallaye a kakar wasan da ta gabata, kyautar da ita ce irinta ta biyar da dan wasan ya taba karba a Tarihi.

Talla

Messi dai ya zura kwallaye 34 ne a wasanni 68 daya bugawa Barcelona matakin inda ya dara takwarorinsa irinsu Salah na Liverpool da kuma Harry Kane na Tottenham.

A bangare guda abokin dabin Messi wato Cristiano Ronaldo da ya lashe kyautar takalmin zinaren har sau 4 ya iya zura kwallaye 26 kadai a wasanni 52 da ya bugawa Madrid.

A tambayoyin da ya amsa daga manema labarai game da wasansu da Lyon a zagayen kungiyoyi 16 na gasar zakarun Turai, Messi ya ce duk da Lyon ba ta cikin manyan kungiyoyin Turai amma tunkararsu abu ne mai hadarin gaske la’kari da irin lallasawar da suka yiwa Manchester City wadda ke matsayin guda cikin manyan kungiyoyin Turai.

A bara ma dai Roma ce ta yi waje da Barcelona a zagayen kungiyoyin 16 batun da ya girgiza magoya bayan kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.