Isa ga babban shafi
wasanni

Jarumar Bollywood ta kwatanta Iwobi da gwaggon biri

Esha Gupta tare da dan wasan Najeriya da ke taka leda a Arsenal Alex Iwobi
Esha Gupta tare da dan wasan Najeriya da ke taka leda a Arsenal Alex Iwobi new18

Fitacciyar Jarumar fina-finan Bollywood na India, Esha Gupta na shan caccaka daga magoya bayan Kungiyar Kwallon Kafa ta Arsenal sakamakon kalaman nuna wariyar launin fata da ta furta kan dan wasan Najeriya da ke taka leda a Arsenal, Alex Iwobi da ta bayyana shi a matsayin gwaggon biri.

Talla

Gupta wadda masoyiyar Arsenal ce ta hakika, ta wallafa hoton tattaunawar da ta yi da wani a shafinta na Instagram, in da ta bayyana Iwobi a matsayin gwaggon biri.

Hakan kuma na zuwa ne sakamakon kashin da Arsenal ta sha a hannun Manchester United a gasar FA a ranar Juma’ar da ta gabata.

Kazalika Jarumar wadda ke yawan ziyartar birnin Londo domin kallon wasan Arsenal kai tsaye, ta yi korafi kan rashin ajiye Iwobi a banci, yayin da ta bayyana shi a matsayin shirmammen dan wasa.

Sai dai tuni magoya bayan Arsenal har ma da mahukuntan kungiyar suka mayar ma ta da martani, in da suka nuna rashin amincewarsu da furta ire-iren wadannan kamalai masu raba kawunan jama’a.

Tuni Gupta ta share hoton kalaman na kaskanci bayan ta sha caccaka, yayin da ta bayar da hakuri.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.