Isa ga babban shafi
wasanni

Ana gab da gano jirgin da ya yi hatsari da Sala

Masu bincike sun ce, babu makawa, Emiliano Sala da matukin jirgin sun mutu
Masu bincike sun ce, babu makawa, Emiliano Sala da matukin jirgin sun mutu LOIC VENANCE / AFP

Rahotanni na cewa, an gano buraguzan jirgin da ya yi hatsari dauke da dan wasan Cardiff City, wato Emiliano Sala.

Talla

Tun a ranar 21 ga watan Janairun da ya gabata ne, jirgin ya yi batan-dabo bayan ya taso daga birnin Nantes na Faransa zuwa Cardiff na Ingila dauke da Sala da matukinsa, David Ibbotson.

Wani lokaci a yau ne ake sa ran masu bincike za su fadada bincikensu a magudanar ruwan da aka gano buraguzan jirgin a Ingila.

Kungiyar kwallon kafa ta Cardiff ta kulla kwantiragi da Sala akan farashin Pam miliyan 15, yayin da wannan ibtila’in ya rutsa da shi a daidai lokacin da yake kan hanyar zuwa kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.