Isa ga babban shafi
wasanni

Manchester City ta rage tazarar makin Liverpool

Sergio Agüero ne ya ci wa Manchester City dukkanin kwallayen uku a karawarsu da Arsenal a Etihad
Sergio Agüero ne ya ci wa Manchester City dukkanin kwallayen uku a karawarsu da Arsenal a Etihad REUTERS/Phil Noble

Kungiyar Kwallon Kafa ta Manchester City ta rage tazarar makin da ke tsakaninta da Liverpool mai jan ragamar teburin fiimiyar Ingila bayan ta lallasa Arsenal da ci 3-1 a Etihad.

Talla

Yanzu haka tazarar maki biyu kacal ke tsakanin kungiyoyin biyu, in da Liverpool ke da maki 61, yayin da Manchester City ke da maki 59.

Sergio Aguero ne ya jefa dukkanin kwallayen uku a ragar Arsenal kuma a karo na 10 kenan da yake ci wa kungiyar kwallaye uku-uku a wasa guda a gasar firimiyar Ingilar.

Yanzu haka, Alan Shearer ne kadai ke gaban Aguero wajen yawan zura kwalleyen uku-uku, in da shi Shearer ya ci wa Manchester City ire-iren wadannan kwalleyen har sau 11 a firimiyar Ingila.

A halin yanzu hankula sun karkata kan fafatawar da Liverpool za ta yi da West Ham United a yau Litinin, yayin da masharhanta ke ganin cewa, watakila Liverpool ta samu nasara musaman idan aka waiwaiyi tarihin cewa, ta samu nasara akan West Ham a haduwa hudu da suka yi a baya-bayan nan.

A bangare guda, kocin West Ham, Manuel Pellegrini ya ce, zai yi kokarin doke Liverpool domin taimaka wa Manchester City yi mata fintinkau a teburi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.