Isa ga babban shafi
Wasanni

Ceferin ya lashe zaben shugabancin hukumar UEFA

Shugaban hukumar UEFA Aleksander Ceferin.
Shugaban hukumar UEFA Aleksander Ceferin. REUTERS/Francois Walschaerts

An sake zabar Aleksander Ceferin a matsayin shugaban hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai UEFA, inda zai shafe shekaru hudu yana jagorancin hukumar.

Talla

Ceferin ya samu nasarar ce a ranar Alhamis yayin babban taron hukumar ta UEFA da ya gudana a birnin Rome.

Yayin zaben shugabancin na UEFA, babu wanda ya kalubalanci aniyar Ceferin ta ci gaba da jagoranci, hakan ya bashi damar lashe zaben cikin sauki.

Shekaru biyu da suka gabata, Aleksander Ceferin ya karbi ragamar jagorancin hukumar UEFA daga Michel Platini dan kasar Faransa, wanda aka samu da laifin aikata laifin yin kwanciyar akan wasu kudade.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.