Isa ga babban shafi
Wasanni

Mai tsaron raga ya suma yayinda ake tsaka da wasa

Mai tsaron ragar kungiyar Napoli David Ospina
Mai tsaron ragar kungiyar Napoli David Ospina AFP/Getty Images

An gaggauta garzayawa da mai tsaron ragar kungiyar Napoli David Ospina asbiti sakamakon faduwa sumamme da yayi, a lokacin da suke tsaka da fafata wasa da Udinese a gasar Seria A ta karshen mako.

Talla

Da fari Ospina yayi karo ne da dan wasan gaba na Udinese Ignacio Pussetto mintuna goma bayan soma wasan, inda ya samu rauni a kansa, amma bayan duba lafiyarsa tare da nada masa bandeji, mai tsaron ragar ya samu komawa wasan.

Sai dai bayan mintuna 41, mai tsaron ragar ya fadi sumamme, abinda yasa aka gagauta garzayawar da shi asibiti, har yanzu kuma ake ci gaba da bashi kulawa.

David Ospina mai shekaru 30, ya zo kungiyar Napoli ne a matsayin aro daga Arsenal .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.