Isa ga babban shafi
Wasanni

Inter Milan ta sanya farashin fam miliyan 68 akan Icardi

Dan wasan gaba na Inter Milan Mauro Icardi.
Dan wasan gaba na Inter Milan Mauro Icardi. REUTERS/Tony Gentile/File Photo

Kungiyar Inter Milan ta sanya farashin fam miliyan 68 kan wasanta na gaba Mauro Icardi, wanda Real Madrid ta dade tana neman sauyin shekarsa zuwa gareta.

Talla

A halin da ake ciki dai, Icardi ya shafe sama da wata guda bai bugawa Inter Milan wasa ba, saboda takaddamar da ke tsakaninsa da kungiyar, kan wasu batutuwa ciki harda yarjejeniyar da ya kulla da ita a baya, hakan tasa a watan Fabarairu kungiyar ta karbe matsayin kaftin dinta da ta bashi.

Rahotanni sun tabbatar da cewa tuni Real Madrid ta tuntubi Inter Milan kan amincewa da biyan farashin da zarar an kawo karshen kakar wasa ta bana.

Tun bayan da Zidane ya sake karbar horar da Real Madrid a makon da ya gabata, kungiyar ta tashi haikan wajen karfafa sashinta na masu jefa kwallo, inda ake sa ran a karshen kakar wasan ta bana, za ta sayi Eden Hazard na Chelsea, sai kuma Mauro Icardi daga Inter Milan, la’akari da cewa, babu tabbas kan makomar yan wasan gaba na kungiyar ta Madrid da suka hada da Karim Benzema da Gareth Bale.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.