Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

FIFA ta dakatar da shirin fadada gasar cin kofin duniya a 2022

Shugaban hukumar FIFA, Gianni Infantino
Shugaban hukumar FIFA, Gianni Infantino REUTERS/Naseem Zeitoon/File Photo

Hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta dakatar da shirinta na fadada kasashen da za su halarci gasar cin kofin duniya ta 2022 zuwa kasashe 48 sabanin 32 da suka saba halarta a baya.

Talla

Abaya dai shugaban hukumar ta FIFA Gianni Infantino ya sanar da cewa sun matso da shirin fadada gasar daga 2026 da aka tsara tun da farko zuwa 2022 inda ya ce Qatar wadda za ta karbi bakoncin gasar za ta hada hannu da takwarorinta kasashen gabas ta tsakiya wajen daukar nauyin gasar don samun wadatattun filayen kwallo.

Sai dai a sanarwar hukumar ta FIFA yau ta ce bayan daukar tsawon lokaci ana tafka muhawara kan batun ta gano cewa ba za a iya fara amfani da sabon tsarin na kasashe 48 a Qatar ba.

Tuni dai hukumar kwallon kafar Qatar ta fitar da sanarwar cewa a shirye ta ke ta karbi kasashen 48 yayin gasar wadda ke tafe nan da shekaru 3 da rabi, sai dai shugaban hukumar kwallon kafar Turai Aleksander Ceferin ya ce abu ne mai wuya kasar ta iya karbar bakoncin kasashe har 48 yayin gasar cin kofin duniyar na shekarar 2022.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.