Isa ga babban shafi
Wasanni

Infantino ya sake darewa shugabancin FIFA wa’adi na 2

Shugaban hukumar FIFA, Gianni Infantino, bayan sake zabarsa a wa'adi na 2 a birnin Paris.
Shugaban hukumar FIFA, Gianni Infantino, bayan sake zabarsa a wa'adi na 2 a birnin Paris. AFP

An sake zabar Gianni Infantino, a matsayin shugaban hukumar kwallon kafa ta Duniya FIFA wa’adi na 2.

Talla

Infantino ya samu nasarar yin tazarce a kujerarsa bayan zaben shugabancin hukumar ta FIFA da aka kammala da safiyar yau laraba a birnin Paris, hakan ke nufin zai ci gaba da shugabantar FIFA har zuwa shekarar 2023.

Yayin zaben dai, baki dayan manyan wakilan hukumar kwalon ta duniya 211 da ke zabar shugaba ne suka goyi bayan ci gaba da shugabancin Infantino, kasancewar shi kadai ne dan takara babu abokin hamayya.

A watan fabarairu na 2016, aka soma zabar Gianni Infantino, mai shekaru 49 a matsayin wanda zai karasa lokacin da tsohon shugaban hukumar Sepp Blatter ya bari, wanda zargin almundahana da cin hanci da rashawa ya daibaibaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.