Isa ga babban shafi
Turai

Shugaban Turkiyya, Erdogan ne abokin ango a auren Ozil

Ozil da shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya
Ozil da shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya Kayhan Ozer/Presidential Palace/Handout via REUTERS

Tsohon dan wasan tawagar kwallon kafar Jamus, wanda yanzu yake wa Arsenal wasa Mesut Ozil ya angwance a yau Juma’a, kuma shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ne babban abokin Ango.

Talla

Dan shekara 30 din wanda yake da usuli da kasar Turkiyya ya janyo cece kuce lokacin da aka ga hotonsa da shugaba Erdogan, lamarin da ya diga ayar tambaya kan karfin kishin kasarsa Jamus, ganin cewa a wayewar garin ranar ce Jamus ta rikito daga gasar cin kofin Duniya ta 2018.

Shugaban na Turkiyya ya isa inda aka yi bikin auren, wato wani otel na kasaita don shaida yadda Ozil zai auri budurwarsa, wacce ta taba zama mace mafi kyau a Turkiyya, Amine Gulse.

An ga Erdogan, wanda yake ta murmushi tare da mai dakinsa Emine tsaye kusa da Ozil da amaryarsa yayin daurin auren.

Bayan ya buga wa Jamus wasanni sau 92, har ma da taka muhimmiyar rawa a lashe kofin duniya a shekarar 2014, kwatsam Ozil ya bayyana yin murabus daga buga wa Jamus wasa a watan Yulin bara, yana mai zargin jami’en hukumar kwallon kafar kasar da nuna masa wariyar launin fata.

A watan Mari na wannan shekarar ya bayyana cewa shugaba Recep Tayyip Erdogan ne babban abokinsa a ranar aurensa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.