Isa ga babban shafi
Wasanni

Gwamnatin Brazil ta kame manyan kadarorin Neymar

Dan wasan kungiyar PSG, Neymar.
Dan wasan kungiyar PSG, Neymar. REUTERS/Lucas Landau

Kalubalen da dan wasan PSG Neymar ke fuskanta ya karu, bayan da hukumar tattara harajin kasarsa Brazil ta kwace gine-ginensa da dama a kasar da wasu kadarori da ya mallaka, saboda samunsa da laifin shafe tsawon lokaci ba tare da ya biya harajin da ake binsa ba.

Talla

Hukumar tattara harajin ta Brazil dai ta bayyana cewa adadin harajin da Neymar ya kaucewa biya ya kai fam miliyan 14,dan hakane ta kwace gine-ginens da sauran kadarori akalla 36.

Sai dai kwace wadannan kadarori ba wai yana nufin Neymar ba zai iya amfani da su bane, yana da damar yin hakan, amma matakin na nufin haramta shi sayar da su ko kuma sanya su cikin wata huldar kasuwanci.

Jami’an tattara harajin Brazil, sun ce tarin harajin da ake bin Neymar na shekarar 2013 ne,lokacin da dan wasan ya sauya sheka daga kungiyar Santos ta kasar zuwa Barcelona.

Almundahanar kin biyan harajin dai kari ne kan matsalolin da Neymar ke fuskanta a baya bayan nan, da suka hada da zargin aikata fyade da wata mata ke yi masa, duk da dai dan wasan ya musanta, sai kuma gargardin da mai kungiyar PSG attajiri Nasser Al-Khelaifi yayiwa dan wasan, na cewa a shirye yake ya sayar da shi, muddin ya ci gaba da nuna rashin da’a, halayyar da a kwanakin baya, ta kai ga Neymar din ya naushi wani dan kallo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.