Isa ga babban shafi
Wasanni

Arsenal ta tuntubi Real Madrid akan Marcelo

Mataimakin kaftin din Real Madrid, Marcelo Vieira da Silva Júnior.
Mataimakin kaftin din Real Madrid, Marcelo Vieira da Silva Júnior. Reuters

Rahotanni daga Spain sun ce akwai kwakkwaran zaton cewa, mataimakin kaftin din Real Madrid, Marcelo, zai sauya sheka zuwa kungiyar Arsenal nan bada dade wa ba.

Talla

Rahoton da jaridar wasanni ta Diario Sport ta rawaito, yace tuni Arsenal ta soma tuntubar Real Madrid don tabbatar da cinikin dan wasan mai shekaru 31.

A baya bayan nan dai kungiyoyin da suka hada da Arsenal, AC Milan, Juventus da kuma PSG, sun bayyana aniyar saye Marcelo daga Real Madrid.

Bayan shafe sama da shekaru 10 a Real Madrid, Marcelo ya taimakawa kungiyar wajen lashe kofuna 20, ciki harda na gasar zakarun kungiyoyin nahiyar Turai guda 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.