Isa ga babban shafi
Wasanni

Barcelona ta yi tayin mika kudi da 'yan wasa 2 kan Neymar

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta PSG Neymar Junior
Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta PSG Neymar Junior Stringer/Reuters

Barcelona ta gabatarwa PSG tayin biyan euro miliyan 40 da kuma mika mata, yan wasanta biyu, Philippe Coutinho da Rakitic don cinikin tsohon dan wasanta Neymar.

Talla

Yunkurin ya zo kwanaki kalilan bayan da Barcelona ta sanar da karbar aron kudi saboda sayen Antoine Griezmann daga Atletico Madrid kan euro miliyan 120, abinda ya jefa yiwuwar komen da Neymar ke son yi zuwa kungiyar ta Barcelona cikin shakku.

A bangaren kungiyar PSG kuwa, tuni ta shaidawa Neymar cewa yana iya rabuwa da ita, amma da sharadin za ta shiga tattaunawa kan sauyen shekarsa ne kawai, idan kudaden da aka yi tayin biya akansa sun kusanci euro miliyan 222, da suka mikawa Barcelona kan dan wasan shekaru biyu da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.