Isa ga babban shafi
Wasanni

UEFA ta bude dandalin zaben kwallo mafi kayatarwa a Turai

Tambarin hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai UEFA, a hedikwatar ta dake birnin Nyon, a kasar Switzerland.
Tambarin hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai UEFA, a hedikwatar ta dake birnin Nyon, a kasar Switzerland. REUTERS/Denis Balibouse/File Photo

Hukumar kwallon kafa ta nahiyar Turai UEFA, ta bude dandalin kada kuri’ar zaben kwallon kafa mafi kayatarwa daga cikin jimillar wadanda aka ci, yayin wasannin nahiyar Turan da suka gudana a kakar wasan da ta gabata.

Talla

Kamar yadda aka saba Lionel Messi da Cristiano Ronaldo ke kan gaba a tsakanin ‘yan wasan da ke takarar lashe kyautar ta zura kwallo mafi kayatarwa, amma a bana, an samu matasan ‘yan wasa da dama da suka bayyana a fagen.

Daga cikin matasan ‘yan wasan da UEFA ta sanya cikin wadanda za ta tantance kayatarwar kwallayen da suka ci a kakar wasa ta bara, akwai Isma’ila Sarr na kungiyar Rennes, Enzo Millot daga kungiyar Monaco da kuma David Faupala na kungiyar Apollon Limassol ta kasar Cyprus.

Kwallon Sarr na Rennes da ke cikin takara it ace wadda ya jefa a ragar FK Jablonec, daga Jamhuriyar Czech yayin gasar Europa a matakin wasannin rukuni.

Shi kuwa Faupala jefa tasa kwallon ce a ragar Lazio, itama a gasar Europa matakin rukuni, yayinda Enzo Millot mai shekaru 17, ya ci tasa kwallon yayin wakiltar Faransa a gasar cin kofin nahiyar Turai, ta ‘yan kasa da shekaru 17.

Idan muka koma kan manyan taurarin kuwa, Kwallon Messi da ta shiga takarar lashe kyautar bara ita ce wadda a jefa a ragar Liverpool yayin karawarsu a gasar zakarun Turai ta hanyar bugun falan daya, yayinda shi kuma Cristiano Ronaldo ya jefa tasa kwallon a ragar Manchester United a gasar ta Zakarun Turai a matakin rukuni.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.