Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Manchester City ta yi nasara kan Liverpool a gasar Community Shield

Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Raheem Sterling, lokacin zura kwallonsa a ragar Liverpool
Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, Raheem Sterling, lokacin zura kwallonsa a ragar Liverpool REUTERS/David Klein

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta yi nasara kan Liverpool a bugun Penalti yayin wasan share fagen tunkarar gasar Firimiya a jiya Lahadi da ya gudana a filin wasa na Wembley.

Talla

Wasan da aka karkare da kwallo daya da daya daga bangarorin biyu, tilas ya sanya bayar da damar bugun daga kai sai mai tsaron raga inda City ta yi nasarar zura dukkanin kwallayenta amma Liverpool ta yi rashin nasarar guda daya da Wijnaldum ya buga inda mai tsaron ragarta Claudio Bravo ya tare.

Raheem Sterling ne dai ya yi nasarar fara zura kwallo daga bangaren City wanda ke matsayin kwallonsa na farko da ya zura ga tsohon Club din nasa Liverpool ko da Alisson Becker ya yi kokarin rike kwallon amma ta subuce daga hannunsa ta shiga raga.

An dai yi tsammanin Liverpool ka iya nasara a wasan ganin yadda har sau 3 Mohammed Salah na kai harin da kiris ya rage kwallo ya shiga raga ciki har da wanda Kyle Walker ya yi gaggawar dawo da ita gab da za ta taba ragar, wato kafin ta ida isa jikin ragar ko kuma dandanin kasa a tsakiyar ragar.

Bisa al’ada dai wasan na Community Shield wanda ke zura mako guda gabanin bude gasar Firimiya duk kudaden shigar da aka samu sanadiyyarsa akan rarrabashi ga mabukata ne a sassan kasar ta Ingila.

Ka zalika wannan wasan shi ne gasa ta farko cikin mabanbantan gasa har 7 da Liverpool za ta fafata a wannan kaka, gabanin bude wasanninta na gasar Firimiya da wasa tsakaninta da Norwich a juma’a mai zuwa kana wasan neman lashe kofin UEFA super Cup da za ta kara da Chelsea ranar Laraba a Istanbul.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.