Isa ga babban shafi

Manchester City na tattaunawa da Juventus don sayen Cancelo

Manajan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola
Manajan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City Pep Guardiola Reuters/Daniel Kramer

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ta ce ta na tattaunawa da Juventus ta Italiya a kokarinta na sayen dan wasanta Joao Cancelo dai dai lokacin da ta ke shirin raba gari da Danilo dan Brazil.

Talla

A cewar Pep Gyardiola wanda bai jima da sayen Kyle Walker kan yuro miliyan 45 ba, ya ce kawo yanzu basu kammala tattaunawa kan makomar ‘yan wasan biyu ba amma suna fatan karkare kulla yarjejeniya kafin karewar wa’adin kasuwar musayar.

Danilo dan Brazil mai shekaru 28 wanda ke son komawa Juventus, City na son maye gurbinsa ne da Cancelo na Juventus mai shekaru 25 dan wasan da ka iya rike baya haka zalika a wasu lokutan ya taka leda a matsayin dan wasan gaba.

A bara ne dai Juventus ta sayo Cancelo daga Valencia kan yuro miliyan 35 kuma ya na cikin tawagar Portugal da ta lashe Kofin Nations League a wannan kaka.

A bangare guda itama City a shekarar 2017 ne ta sayo Danilo daga Real Madrid kan yuro miliyan 26 da rabi kuma ya taimaka wajen nasarar Club din ta dage kofin Firimiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.