Isa ga babban shafi
Wasanni

Kungiyoyin Ingila sun kashe sama da Pam biliyan 1 a kasuwar bana

Kwallon Kafa
Kwallon Kafa Reuters

A yayinda aka rufe kasuwar musayar ‘yan wasa a Turai, kungiyoyin da ke taka leda a gasar firimiya ta Ingila sun kashe jumullar Pam biliyan 1 da miliyan 41 wajen cefanen ‘yan wasan.

Talla

Sai dai wannan adadi bai kai yawan kudaden da kungiyoyin na Ingila suka kashe a shekarar 2017 ba ,inda a wancan lokacin suka kashe Pam biliyan 1 da miliyan 43.

A ranar karshe ta rufe kasuwar musayar ‘yan wasan,wato a jiya Alhamis, manyan kungiyoyin na Ingila sun kashe Pam miliyan 170 amma akan cefanen 'yan wasa 17.

A bangare guda, Everton ta sayi dan wasan Najeriya, Alex Iwobi daga Arsenal akan farashin Pam miliyan 34, daya daga cikin cefene mafi tsoka da aka yi a firimiyar Ingila a bana, yayinda Romelu Lukaku ya koma Inter Milan daga Manchester United akan farashin Pam miliyan 74.

Arsenal ita ce, kungiyar Ingila wadda ta fi lale kudade wajen sayo ’yan wasa a bana, inda ta yi cefanen Pam miliyan 155. A  ranar karshe ta rufe kasuwar, Arsenal ta sayo Kieran Tierney daga Celtic akan Pam miliyan 25, sannan kuma ta sayi David Luiz daga Chelsea akan Pam miliyan 8.

Cefanen Harry Maguire daga Leicester City zuwa Manchester United, shi ne mafi tsoka a Ingila a bana, inda aka sayar da shi akan Pam miliyan 80, yayinda  cefenen Nicolas Pepe daga Lille zuwa Arsenal akan farashin Pam miliyan 72, ke cikin manyan musaya da aka yi.

Manchester City ta sayi Rodri daga Atletico Madrid akan farashin Pam miliyan 62.8, da kuma Joao Cancelo daga Juventus akan farashin Pam miliyan 60.

Tottenham ta kashe Pam miliyan 53.8 wajen sayo Tanguy Ndombebe daga Lyon.

Kadan kenan daga cikin manyan cefanen da aka yi wajen sayo ‘yan wasa a Ingila a kasuwar bana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.