Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

United ta antaya wa Chelsea kwallaye 4 a wasan farko

Marcos Rashford, dan wasan Manchester United
Marcos Rashford, dan wasan Manchester United REUTERS/Peter Powell

Marcus Rashford ya ci kwallaye biyu yayin da manchester United ta lallasa Chelsea da ci 4-0 a gasar Firimiyar Ingila da ta fara da kafar dama a ranar Lahadi.

Talla

Dama ‘yan wasan na koch Ole Gunnar Solskjaer na neman abin da zai huce musu takaici sakamakon munanan sakamakon da suka samu a kakar da ta gabata.

Rashford ya fara ci wa Manchester United kwallo ne a wasan daga bugun daga – kai – sai – mai –tsaron – gida, kafin daga bisani kwallaye uku suka samu bayan hutun rabin lokaci cikin mintuna 16 ta hannun Anthony Martial, Rashford, da sabon dan wasa Daniel James.

Su ma sabbin ‘yan wasan baya na Manchester United, Harry Maguire da Aaron Wan-Bissaka sun baiwa mara – da kunya a wasan, lamarin da ya sa ake ganin kwalliya ta biya kudin sabulu, duk da cewa an kashe fam miliyan 130 wajen sayen su biyu.

Wannan ne wasan farko da sabon kocin Chelsea Frank Lampard ya jagoranci kungiyar a matsayin mai horarwa, inda ya yi karfin hali wajen farawa da matasa kamar Tammy Abraham da Mason Mount.

Baya ga dakatar da Chelsea daga sayen ‘yan wasa a kasuwan cinikin ‘yan wasa na wannan kaka, akasarin manyan masu murza tamaula a kungiyar suna fama da rauni, amma Lampard bai kawo hakan a matsayin hujja ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.