Isa ga babban shafi

Ronaldo ya biya Mayorga kudi don shafe zarginsa da yi mata fyade

Cristiano Ronaldo
Cristiano Ronaldo REUTERS/Rafael Marchante

Cristiano Ronaldo na Portugal da ke taka leda a Juventus ya amince da jita-jitar da ke nuna cewa ya bai wa Kathryn Mayorga tsabar kudi har dala dubu dari 375 sai dai ya musanta cewa ya yi hakan ne don kulle mata baki game dazargin Fyaden da take masa a shekarar 2009.

Talla

Cikin jawaban lauyoyin Ronaldo a gaban kotu can Amurka dake neman korar karar, sun bayyana cewa dan wasan ya baiwa Mayorga kudaden ne don sanyaya mata rai tare da kawo karshen zargin inda kuma tuni ta sanya hannu don janye karar da ta ke.

A cewar lauyoyin na Ronaldo tun a shekarra 2018 Mayorga ta karbi kudaden yayin da sanya hannu kan yarjejeniyar janye karar.

Tawagar lauyoyin na Ronaldo dai sun bukaci kotu ta yi amfani da yarjejeniyar wajen kawo karshen shari’ar.

Tun a shekarar 2010 shekara ne Mayorga ta zargi Ronaldo da yi mata fyade a wani dakin Otel da ke Las Vegas ta Amurka, sai dai dan wasan na ci gaba da musanta batun, inda ya ce kawo yanzu babu gamsasshiyar hujjar da ke nuna ya aikata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.