Isa ga babban shafi
Wasanni

PSG da Barcelona sun gana kan cinikayyar Neymar

Neymar na Brazil
Neymar na Brazil REUTERS/Benoit Tessier

Hukumomin PSG da Barcelona sun gana a birnin Paris na Faransa a wannan Talata domin tattaunawa kan yiwuwar cimma yarjejeniyar cinikayyar Neymar na Brazil.

Talla

Rahotanni na cewa, kungiyoyin biyu sun gamsu da tattaunawar da ta gudana a tsakaninsu duk da cewa, akwai dimbin abubuwan da ba su gama cimma matsaya akan su ba.

Neymar mai shekaru 27, ya koma PSG ne daga Barcelona a shekarar 2017 akan farashin Euro miliyan 222, yayinda a yanzu Barcelona ke son maido da shi Camp Nou.

Barcelona ta gabatar ta tayin Euro miliyan 170 a matsayin farashin sayo Neymar daga PSG.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.