Isa ga babban shafi
Wasanni

Super Eagles ta shiryawa wasansu da Ukraine

Tawagar 'yan wasan Najeriya ta Super Eagles
Tawagar 'yan wasan Najeriya ta Super Eagles REUTERS/Dylan Martine

Tawagar kungiyar kwallon kafar Najeriya, Super Eagles ta fara atisayen tunkarar wasan sada zumunta tsakaninta da Ukraine a gobe Talata bayan isarta Dnipro tun a shekaran jiya Asabar.

Talla

Wasan wanda zai gudana da misalin karfe 7:30 agogon Najeriya a babban filin wasa na Dnipro mai daukar mutane dubu 31, rahotanni sun bayyana cewa ilahirin ‘yan wasan da za su taka leda a kwallon sun hallara ciki har da wadanda aka gayyato sakamakon uzurin da wasu ‘yan wasan suka bayar na gaza halarta.

Yanzu haka dai ‘yan wasa irinsu Francis Uzoho, Ikechukwu Ezenwa da William Troost-Ekong da Jamilu Collins, da Leon Balogun, dakuma Bryan Idowu, baya ga Alex Iwobi, Joseph Aribo, da Oghenekaro Etebo da kuma Anderson Esiti sun hallara a fili.

Sai sabbin ‘yan wasan da aka gayyato wadanda suka kunshi Joshua Maja da Samuel Kalu da Paul Onuachu da kuma Victor Osimhen baya ga Samuel Chukwueze, da Emmanuel Dennis da Moses Simon suma dukkanninsu sun hallara.

A bangaren Super Eagles dai wasan na matsayin atisayen tunkarar wasanninta na neman gurbin shiga gasar cin kofin Afrika a shekarar 2021 wasannin da za ta kara da jamhuriyar Benin da kuma Lesotho gabanin samun gurbi a gasar wadda a wannan karon ta karkare a matsayin ta 3 kasa da Senegal da ke matsayin ta 2 da kuma Algeria da ke rike da kofin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.