Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Ronaldo ne ya cancanci kyautar gwarzon dan kwallon duniya - Juventus

Cristiano Ronaldo dan wasan Juventus da Portugal
Cristiano Ronaldo dan wasan Juventus da Portugal Susana Vera/Reuters

Daraktan wasanni na kungiyar kwallon kafa ta Juventus, Fabio Paratici ya ce Cristiano Ronaldo ne ya kamata ya lashe kyautar gwarzon dan nkwallon kafa na Duniya.

Talla

Kamar yadda aka sani dai dan wasan Barcelona, Lionel Messi ne ya lashe kyautar a bikin da ya gudana a Milan na kasar Italiya, inda Virgil van Dijk ya zo na biyu, Ronaldo na uku.

Sai dai jami’in na Juventus yana gani FIFA ta yi kuskure a hukuncin da ta yanke, saboda Ronaldo ne ya cancanci kyautar, duba da lambobin yabon da ya samu a shekarar da ake la’akari da ita.

Ronaldo ya samu maki 36, wadda hakan ya sa Messi mai maki 46 Van Dijk mai 38 suke gabansa a kyautar da ake la’akari da kuri’un da kaftin da kocawa na tawagogin kwallon kafar kasashe da kuma wakilan kafafen yada labarai ke kadawa.

Yayin da Messi ya zabi Ronaldo a matsayi na biyu a kuri’ar da ya kada, Ronaldo bai ma zabi Messi ba.

Zalika, Ronaldo bai halarci bikin bayar da kyautar da ya gudana a La Scala Opera House na Milan ba, sanna kuma bai fafata a wasan Juventus da Brescia ba a ranar Talata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.