Isa ga babban shafi
Wasanni

Har yanzu ni ba Galatico ba ne- Hazard

Eden Hazard na Real Madrid
Eden Hazard na Real Madrid © REUTERS/Sergio Perez

Eden Hazard na Real Madrid ya ce har yanzu, ba ya kallon kansa a matsayin Galatico. ‘Galatico’ kalma ce da ake amfani da ita kan dan wasan da Real Madrid ta saya da makuden kudade wanda kuma ke da kwarjini a duniyar tamaula.

Talla

Hazard ya fadi haka ne bayan da Madrid ta saye shi akan Euro miliyan 150 daga Chelsea, amma kawo yanzu bai zura kwallo ko guda ba a wasanni uku da aka fara da shi a gasar La Liga ta Spain.

Ana kallon Hazard mai shekaru 28 a matsayin magajin Cristiano Ronaldo, inda har ma aka ba shi riga mai lamba 7 da Ronaldo ya sanya kafin barinsa Madrid zuwa Juventus.

Sai dai har yanzu, Hazard bai nuna kansa ba kamar Ronaldo, abin da watakila yake ganin har yanzu bai cancanci a kira shi ‘Galatico’.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.