Isa ga babban shafi
Wasanni-Tennis

Japan Open: Djokovic ya kai matakin daf - da - na - kusa - da - karshe

Novak Djokovic
Novak Djokovic RFI/Pierre René-Worms

Novak Djokovic ya yunkuro a jiya Laraba a gasar kwallon Tennis ta Japan Open, inda ya wargaza babban kalubalensa, Go Soeda da ci 6-3 7-5 ya tsallaka zuwa matakin daf – da – na – kusa – da - karshe.

Talla

Dan wasan, wanda shine lamba daya a duniya ya ce yana jin radadi a kafadarsa da ya ji raunin da ya hana shi fafatawa a gasar US Open, yayin da yake shirin karawa da dan wasan Faransa, lamba 5 a duniya Lucas Pouille a filin Ariake Coloseum, inda za a yi gasar Olympic ta Tokyo a 2020.

Djokovic na cikin samun nasara ne sai kwatsam dan kasar Japan din mai shekaru 35 da suke karawa ya kara azama, ya zame wa Djokovic alakakai, har wasan da yake 5-3 ya kasance 5-5, sakamakon kurakuran da lamba dayan ya dinga yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.