Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Barcelona ta kori Valdes

Victor Valdes lokacin da yake tsaron ragar Barcelona
Victor Valdes lokacin da yake tsaron ragar Barcelona Javier Segura/Wikimedia Commons

Barcelona ta sallami kocin tawagar matasan ta ta ‘yan kasa da shekaru 19 Victor Valdes ba tare da bata lokaci ba, bayan rade – radin sa – in – sa tsakaninsa da daraktan matasa na kungiyar Patrick Kluivert.

Talla

A watan Yulin wannan shekarar Valdes ya koma Barcelona don jan ragamar karamar tawagar, shekaru biyar bayan ya bar kungiyar a matsayinsa na mai tsaron raga.

Dan shekara 37 ya kasance cikin jiga –jigan tsaffin ‘yan wasan kungiyar bayan shekaru 12 masu cike da nasara da ya yi a kungiyar, in da ya ci kofunan La Liga 6 da na zakarun Turai 3.

Rahotanni na cewa ba Kluivert ne kawai mutumin da ke gutsiri – tsoma da Valdes ba a kwanaki 80 da ya yi yana jan ragamar tawagar, sauran jami’ai ma ba sa jin dadin yadda yake tafiyar da harkokin atisaye.

An kara tada jijiyoyin wuya lokacin da tsohon mai tsaron ragar Spain din ya zake cewa za ayi salon wasan wasa na 4-4-2 maimakon 4-3-3 da take amfani da shi a matakin matasa.

Patrick Kluivert da Victor dukkanninsu tsaffin ‘yan wasan Barcelona ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.