Isa ga babban shafi
Wasanni

Saura kiris na rabu da Barcelona saboda bacin rai - Messi

Lionel Messi.
Lionel Messi. REUTERS/Albert Gea

Gwarzon kwallon kafa na duniya Lionel Messi, ya ce kiris ya rage ya rabu da kungiyarsa Barcelona gami da daina taka leda a Spain ma baki daya, lokacin da ya fuskanci matsin lamba gami da bincike kan zargin kin biyan haraji.

Talla

Yayin kakar wasa ta 2013/2014 Messi da mahaifinsa Jorge suka soma fuskantar tuhuma daga hukumar tara harajin Spain, bayan da ta same su da laifin kin biyan harajin da adadinsa ya kai euro miliyan 4 da dubu 100, a tsakanin shekarun 2007 zuwa 2009.

Bayan tabbatar da laifin ne Messi da mahaifinsa suka biya tarar euro miliyan 10, aka kuma yankewa dan wasan hukuncin daurin watanni 21 a gidan Yari, to sai dai an jingine zartas da hukuncin daurin sakamakon afuwar da aka yi masa.

Yayin zantawa da manema labarai Messi ya ce ba shakka a waccan lokacin Barcelona ta fita daga ransa, amma a halin yanzu ya shirya karkare wasansa a kungiyar, inda yarjejeniyarsa za ta kare 2021, wadda ya ce yana iya tsawaita wa’adinta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.