Isa ga babban shafi
Wasanni

Barcelona ta soma laluben wanda zai maye gurbin Suarez

Dan wasan gaba na Barcelona Luis Suarez.
Dan wasan gaba na Barcelona Luis Suarez. REUTERS/Sergio Perez

Rahotanni daga Spain sun tabbatar da cewa, kungiyar Barcelona ta soma nazari kan maye gurbin mai jefa mata kwallo, Luis Suarez da Victor Osimhen, dan Najeriyar dake haskawa a kungiyar Lille dake gasar League 1 a Faransa.

Talla

Barcelona ta dade tana laluben wanda zai iya maye mata gurbin Suarez, dan wasanta na gaba da a badi zai cika shekaru 33.

Wasu karin yan wasan kuma da Barcelonan ke bibiyar lamuransu kan yiwuwar shawarar ta maye gurbin Suarez sun hada da, Kylian Mbappe, Harry Kane, Marcus Rashford ko kuma Lautaro Martinez na kungiyar Inter Milan.

Bayan sauya sheka daga Liverpool zuwa Barcelona a shekarar 2014, Suarez ya ci wa kungiyar kwalaye 164, a wasanni sama da 2 da 20 daya buga mata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.