Isa ga babban shafi
Wasanni-Tennis

Federer zai fafata a gasar Olympic ta 2020

Roger Federer a gasar Roland Garros
Roger Federer a gasar Roland Garros REUTERS/Vincent Kessle

Shahararren dan wasan kwallon Tennis, Roger Federer ya bada tabbacin cewa yana da niyyar fafatawa a gasar Olamfik ta shekarar 2020 da za ta gudana a Tokyo ta Japan, a kokarinsa na lashe lambar zinare da take nema ta gagare shi.

Talla

Babban dan wasan dan kasar Switzerland, wadda a lokacin gasar zai cika shekara 39 da haihuwa,yana daga cikin ‘yan wasan kwallon Tennis da suka shahara a duniya, suka kuma lashe lambobi da dama, amma bai tabac in lamabar zinare a Olamfik ba.

A shekarar 2012 a Landan, Federer ya ci azurfa bayan takwaransa na Birtaniya Andy Murray ya doke shi a wasan karshe.

‘’A karshe dai na yanke shawarar fafatawa a wannan gasa ta Olamfik kuma’’ inji Federer.

Federer, wadda bai samu zuwa gasar da aka yi a Rio ta kasar Brazil ba sakamakon rauni da ya ji a shekarar 2016, ya taba cin lambar zinare amma ta ‘yan wasa biyu shi da Stan Wawrinka.

A gasar ta kowa –ta – shi – ta fishe – shi, Federe ya kare a matsayi na 4 a shekarar 2000 a Sydney, sannan aka yi waje da shi a zagaye na biyu a shekarar 2004 a birnin Athens, a Beijin ya kai wasan daf –da – na – kusa – da – karshe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.