Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Akwai yiwuwar Ozil ya bar Arsenal kafin 2021

Dan wasan Arsenal Mesut Ozil
Dan wasan Arsenal Mesut Ozil REUTERS/Eddie Keogh

Wata majiyar wasanni a Ingila ta bayyana cewa mai yiwuwa dan wasan tsakiya na Arsenal Mesut Ozil ya raba gari da Club din gabanin kammaluwar kwantiraginsa a shekarar 2021.

Talla

Ozil wanda yanzu haka ya ke fuskantar bancawa daga Mai horar da kungiyar ta Arsenal Unai Emery wasanni biyu kacal ya doka cikin wannan kaka, a jumullar mintuna 142.

Sai dai duk da matakin Emery na banca Ozil kocin ya bayyana dan wasan mai shekaru 31 a cikin jerin Kaftin din Arsenal 5

Akwai dai jita-jitar da ke nuna cewa Arsenal da kanta na son rabuwa da Ozil yayin kasuwar musayar ‘yan wasa ta watan Janairu, yayinda shima daga bangarensa wata majiya ke bayyana cewa yana shirye-shirye komwa Turkiya da takaleda.

Sai dai dan wasan a zantawarsa da jaridar wasanni ta Birtaniya ya bayyana cewa yana fatan kammala kwantiraginsa gabanin barin Club din.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.