Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Laliga ta daukaka kara kan wasan Classico

Wasan Classico tsakanin Real Madrid da Barcelona
Wasan Classico tsakanin Real Madrid da Barcelona REUTERS

Hukumar Laliga ta ce za ta daukaka kara game da matakin hukumar kwallon kafar Spain na sanya ranar 18 ga watan Disamba a matsayin ranar da wasan Classico tsakanin Real Madrid da Barcelona zai gudana.

Talla

A jiya Laraba ne dai hukumar kwallon kafar Spain ta fitar da ranar wanda ta ce ya biyo bayan cimma jituwa tsakanin kungiyoyin kwallon kafar 2.

Sai dai Laliga ta bayyana cewa ya sabawa kwanakin da ta gabatar na ko dai 4 ko kuma 7 ga watan na Disamba.

Sanarwar da Laliga ta fitar a yau Alhamis ta ce bata gamsu da matakin gudanar da wasan ranar 18 ga watan Disamba ba, a don haka za ta daukaka kara don sauya matakin.

A cewar Laliga, ita ke da damar sanya ranar da wasan zai gudana hasalima ranar ta 18 ga watan Disamba ta zo dai dai da wasan Copa Del Rey.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.