Isa ga babban shafi
Wasanni

Zidane ya musanta rahoton cewa Bale na shirin rabuwa da Madrid

Zinedine Zidane.
Zinedine Zidane. REUTERS/Juan Medina

Mai horas da Real Madrid Zinaden Zidane, yayi watsi da rahotannin da ke cewa dan wasansa na gaba Gareth Bale na gaf da barin kungiyar, abinda yasa a litinin din da ta gabata, dan wasan yayi tattaki zuwa birnin London don ganawa da wakili ko dillalinsa.

Talla

Yayinda yake Karin bayani kan halin da ake ciki, Zidane ya ce, Real Madrid ce a hukumance ta baiwa Bale damar tafiyar da yayi zuwa London, domin wasu bukatu da suka shafi rayuwarsa.

Ce-ce-kuce kan makomar Gareth Bale a Real Madrid ta sake tashi ne, bayan da rahotanni suka ce, dan wasan na Wales ya bukaci kungiyar tasa da kada ta wallafa bayanan lafiyarsa, saboda yana da damar kin amincewa da wallafa bayanan kamar yadda doka a Spain ta zayyana.

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da jaridar Marca ta ce, kungiyar kwallon kafa ta Shanghai Shenhua ta sake yunkurawa domin sayen Bale daga Real Madrid.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.