Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Barcelona ta maye gurbin Valverde da Quique Setien

Tsohon Kocin Barcelona Ernesto Valverede tare da sabon koci Quique Setien.
Tsohon Kocin Barcelona Ernesto Valverede tare da sabon koci Quique Setien. Kanyidaily.com

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta sanar da sunan Quique Setien a matsayin wanda zai maye gurbin Ernesto Valverde da ta kora a bakin aiki jiya Talata.

Talla

Ververde mai shekaru 55, ya taimakawa Barcelona dage kofin Laliga har sau 2 yayinda a yanzu haka ta ke matsayin jagora a teburin gasar ko da dai banbancin kwallo ne kadai tsakaninsu da Real Madrid babbar abokiyar dabinsu.

Cikin sanarwar da Club din ya wallafa ya ce sun cimma matsaya tsakaninsu da tsohon mai horarwa Ververde wanda ya amince da ajje aikinsa yayinda Setien mai shekaru 61 kuma tsohon mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Real Betis ya amince da kulla kwantiragin shekaru 2 da rabi.

Velverde wanda tun daga kakar wasan data gabata suka fara fuskantar takun saka biyo bayan sanya rai da Barcelonar ta yi na kaiwa wasan karshe a gasar cin kofin Turai amma Liverpool ta baro ta, Club din ya bayyana cewa babban fatansa a wannan karon shi ne lashe kofin zakarun Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.