Isa ga babban shafi
Wasanni-Tennis

Serena Williams ta sha kashi a Australian Open

Serena Williams.
Serena Williams. Reuters/Geoff Burke

‘Yar wasan kwallon tennis ‘yar kasar Amurka, Coco Gauff mai shekaru 15 ta gwada cewa nasarar da ta samu kan Venus Williams a shekarar da ta gabata ba tsabagen katari bane, yayin da ta doke abokiyar karawarta, ’yar gidan Williams, wacce sau 7 ta taba lashe babbar kofi Grand Slam, Serena Williams, lamarin da ya kai ta zagaye na biyu na gasar Australian Open.

Talla

A watan Yulin shekarar da ta gabata ne aka fara jin duriyar Gauff a harkar tennis ta duniya bayan ta samu nasara kan ‘yar wasan da take matukar birgeta, Venus Willliams mai shekaru 39 a zagaye na farko a gasar Wimbledon, kuma kamar yadda aka yi a bara, ta doketa kai tsaye da ci 7-6 (7-5) 6-3.

Sai da Gauff ta jinkirta murnar samun nasara saboda ba ta ma san an ba ta maki na karshen ba.

A karon farko kenan Gauff ta samu damar karawa a wannan mataki a wannan babbar gasa sakamakon banjitar da ta nuna a gasar Wimbledon ta bara.

Bajintar da ta yi a Wimbledon ne ma ya sa ‘yan kallo a filin wasa na Margaret Court Arena suka nuna mata sanayya da soyayya yayin karawarta da wacce ta taba zama lamba daya a kwallon tennis a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.