Isa ga babban shafi
Wasanni-Tennis

Djokovic da Federer zasu gwada kwanji a Australia Open

Lamba daya a kwallon Tennis a duniya, Novak Djokovic yayin da ya lashe kofin Paris Masters a 2019.
Lamba daya a kwallon Tennis a duniya, Novak Djokovic yayin da ya lashe kofin Paris Masters a 2019. REUTERS/Christian Hartmann

A gasar kwallon Tennis da ke ci gaba da gudana a kasar Australia, wato Australia Open, za a yi karon batta tsakanin shahararrun ‘yan wasa, Roger Federer da takwaransa Novak Djokovic a matakin kusa da karshe, wato semi finals, kuma haduwa na 50 kenan tsakanin zakakuran ‘yan wasan a yau Alhamis.

Talla

A wannan karon dai dan kasar Switzerland Federer ne a kasa, saboda zai kara ne da lamba daya na duniya mai ci a kwallon Tennis, wato Djokovic a birnin da ake sa ran yanayin zafi ya kai digiri 37 a ma’aunin Celsius, ko kuma 99 a ma’aunin Fahrenheit.

A haduwan da ‘yan wasan suka yi a tsakaninsu har sau 49, Djokovic mai shekaru 32 ne ke kan gaba, inda sau 26 ya doke Federer, inda Federer ya samu galaba a kansa sau 23; kuma yayin da a cikin sauki Djokovic ya samu kaiwa matakin kusa da na karshe, da kyar da jibin goshi Federer ya samu kaiwa matakin. .

Sai dai Djokovic ya ce bajintar da Federer ya nuna a haduwarsa da John Millman, lamba 100 a duniya ne ma dalilin da ya sa dole a ji tsoron karo da shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.