Isa ga babban shafi
Wasanni-Kwallon kafa

Man City ta kai wasan karshe na kofin Carabao

Kocin City Pep Guardiola.
Kocin City Pep Guardiola. REUTERS/Gleb Garanich

Mai horar da ‘yan wasan tawagar Manchester City, Pep Guardiola ya ce dole ‘yan wasansa su koyi yadda za su ci gaba da kasancewa masu amince da nagarta bayan da suka kai matakin wasan karshe karo na 3 a jere da kyar a gasar cin kofin Carabao.

Talla

Tawagar Guardiola zata barje gumi da Aston Villa a filin wasa na Wembley a ranar 1 ga watan Maris mai zuwa duk da rashin nasarar da ta yi a karonta da Manchester United, inda wasa ya tashi 3-2 jimilla.

Manchester City ke kan gaba da ci 3-1 bayan lallasa United a haduwar farko a filin wasa na Old Trafford, kuma a karawa ta biyu a daren Laraba, sun yi ta kokarin kwance wa Manchester United zani a kasuwa a filin Etihad amma mai tsaron raga David de Gea ya cire wa tawagarsa kiste a wuta.

Akasin yadda aka yi zato, United ce ta saka kwallo a ragar City kafin hutun rabin lokaci inda tsohon dan wasan Chelsea, Nemanja Matic ya debe wa kocinsa Ole Gunnar Solksjaer takaici wajen jefa wannan kwallo a raga a yunkurin farko.

Kocin City Guardiola ya ce, a ta kowane fanni sun fi United kyau a sama da mintuna 180 da suka gwada kwanjinsu, saboda sun samar da damammaki na cin kwallaye amma suka kasa amfani da su, saboda haka yake cewa akwai bukatar ‘yan wasansa su koyi yadda za su ci gaba da kasancewa da aminci da azanci a gaban raga.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.